Afrika Ta Kudu, Ta Karbi Kashin Farko Na Allurar Rigakafin Korona

2021-02-02 09:25:18
Afrika Ta Kudu, Ta Karbi Kashin Farko Na Allurar Rigakafin Korona

Kasar Afrika ta kudu, ta karbi kashin farko na riga kafin cutar korona daga kamfanin harhada magunguna na AstraZeneca dake reshe a Indiya.

Shugaban kasar Cyril Ramaphosa, ya bayyana hakan a matsayin wani abu mai kwantyar da hankali a kasar data fi fama da cutar korona a nahiyar afrika.

Ya kuma bayyana hakan da babban ci gaba a matakin yaki da annobar a kasar.

Nan da makwanni biyu ne ake sa ran kaddamar da shirin yi wa jama’ar kasar rigakafin, wanda za’a soma da yi wa ma’aikatan lafiya.

Afrika ta kudu, it ace wata kasa a nahiyar AFrika data fi fama da yawan masu cutar korona, inda kawo yanzu mutane miliyan 1, 453, 761 ne suka harbu da cutar, sai kuma sama da 44,000 data yi ajalinsu a cewar alkalumman da kamfanin dilancin labaren AFP, ke fitarwa kan masu kamuwa da cutar a duniya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!