An Fara Tattaunawa Ta Tsakanin ‘Yan Libiya A Geneva

2021-02-02 09:20:31
An Fara Tattaunawa Ta Tsakanin ‘Yan Libiya A Geneva

Tawagogi daga bangarori daban daban na Libiya, sun fara wata tattaunawa game da makomar kasar a birnin Geneva.

Za’a kwashe mako guda bangarorin na tattaunawa domin zabar sabon firaminista da kuma mambobin majalisar zartaswa da zata yi rikon kwarya kafin zabubukan kasar a watan Disamba.

Saidai a baya baya nan ana nuna shakku game da batun samar da zaman lafiya a kasar a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a birnin Tripoli, duba da rikicin da ya kunno kai tsakanin firaministan kasar mai murabus, Fayez el-Sarraj, da ministan cikin gida na kasar Fathi Bachagha, wanda ake ganin zai iya zama sabon firaministan kasar.

Tuni dai kungiyar ICG, dake sanya ido kan rikice rikice a duniya, ta yi gargadi game da rashin samun fahimtar juna tsakanin bangarorin ‘yan siyasar na Libiya, a wannan tattaunawar, wanda a cewar kwararun kungiyar dukkan bangarorin na da karfin siyasa, soji da kuma kudi, domin wargaza tattaunawar ta Geneva ta hanyar kin amincewa da zaben ko sakamakonsa.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!