​Khadib Zade:Iran Ba Zata Tattauna Kai Tsaye Da Amurka Ba

2021-02-01 19:52:03
​Khadib Zade:Iran Ba Zata Tattauna Kai Tsaye Da Amurka Ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sa’id Khadib Zade ya bayyana cewa mataki na farko wanda yakamata gwamnatin Amurka mai ci ta dauka shi ne dage dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar Iran, sannan ta koma cikin yarjejeniyar JCPOA. A nan ne take da damar tattaunawa da kasar Iran bisa iyakokin da yarjejeniyar nukliyar kasar ta shekara ta 2015 ta shimfida.

Majiyar muryar JMI ta nakalto Khadib Zade ya na fadar haka a safiyar yau Litinin ya kuma kara da cewa dole ne gwamnatin Amurka ta aiwatar da alkawuran da ta dauka a yarjejeniyar JCPOA da kuma kudurin MDD mai lamba 2231.

Ya kuma kara da cewa kasar Iran ce ta raya yarjejeniyar JCPOA tare da amfani da maddoji 26 da 36 na yarjejeniyar.

Dangane da ziyarar aiki wanda Jami’an kungiyar Taliban ta kasar Afganistan suka kawo nan Tehran makon da ya gabata kuma, Khadib Zade ya ce gwamnatin kasar Iran tana bukatar zaman lafiya mai dorewa a kasar Agnasitan, wanda kuma zai samu ne kawai tare da hadin kan mutanen kasar, daga ciki har da kungiyar Taliban.

Kafin haka gwamnatin ta bayyana cewa ba zata taba amincewa da duk wani bangare na kasar Afganistan wanda ya kwaci iko da karfi ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!