Mauritania:Malaman Addini Kimani 200 Ne SuKa Fidda Fatawar Haramta Hulda Da Isra’ila

2021-02-01 19:48:50
Mauritania:Malaman Addini Kimani 200 Ne SuKa Fidda Fatawar Haramta Hulda Da Isra’ila

A dai dai lokacinda majalisar dokokin kasar Mauritania take kira ga gwamnatin kasar, ta kafa dokar haramta hulda da Isra’ila, manya-manyan malaman addini a kasar kimani 200 ne suka fidda fatawar haramta hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila (HIK) a matsayin mahangar addinin musulunci.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa malaman sun amince da wannan fatawar ce a wani taron da suka gudanar a masallacin “Taufik” da ke birnin Nuwakshot babban birnin kasar. Malaman sun kara da cewa hulda da HKI goyon baya ne ga ta’asan da take aikatawa a kasar Palasdinu mai tsari, da kuma kisa da rushe rushen gidajensu da take yi.

Kafin haka dai wasu kafafen yada labarai na HKI da kuma Amurka sun bada labarin cewa kasashen Mauritania da Indonasia ne zasu cikin jerin kasashen Larabawa da musulmin, wadanda za su samar da hulda da HKI nan gaba. Bayan kasashen UAE, Bahrain, Sudan da kuma Morocco.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!