Iran: Hukumar Gidajen Radiyo Da Talabijin Ta Kasa Ta Sami Lambobin Yabo A Nahiyar Asia

Labaran da hukumar radoyi da talabijin ta kasar Iran (IRIB) ta aika zuwa bikin baje kolin labarai na kungiyar gadajen radiyo da talabijin ta kasashen Asia (ABU) sun sami lambobin yabo da dama.
Kamfanin dillancin labarai na kasar Iran, IRAN PRESS ya
bayyana cewa an aike da labarai kimani dubu guda zuwa gasar baje kolin labaran,
wacce ake kira ASIAVISION a takaice. Inda alkalan gasar suka zabi labarai guda
100 mafi muhimmanci da janhakali, wadanda kuma suka hada da labaran da IRIB ta
wallafa da dama.
Labarin ya kara da cewa IRIB ta zama zakara a bangaren labarai
da dumi duminsu, sannan a bangarori biyu
na ‘labarai masu rahotanni’ sai kuma a matsayin zakara a labarai cikin hotuna.
An kafa hukumar ASIAVISION ne a shekara 1984 inda gidajen
radiyo da talabijin na kasashen Asiya da Pacific suke musayar labarai ma su
muhimmanci a tsakaninsu a ko wace rana.
An fara gasar baje kolin labaran ne ta yanar gizo a ranar 27
ga watan Jenerun da ya gabata saboda matsalar cutar korona da ta addabi
kasashen duniya.