​Faransa Ta Bukaci Jamus Ta Dakatar Da Aikin Shimfida Bututun Gas Daga Kasar Rasha

2021-02-01 19:36:09
​Faransa Ta Bukaci Jamus Ta Dakatar Da Aikin Shimfida Bututun Gas Daga Kasar Rasha

Gwamnatin kasar Faransa ta bukaci kasar Jamus ta dakatar da aikin shimfida bututun gas daga kasar Rasha, wato aikin da ake kira ‘Nord Stream 2 Projct’ saboda nuna fushinta dangane da tsare fitaccen dan adawar kasar ta Rasha mai samun goyon bayan kasashen yamma, Alexei Navalny.

Ministar harkokin tarayyar turai na kasar Faransa, Clement Beaune ne ya yi wannan kirar a safiyar yau litinin. Ya kuma kara da cewa kasashen na Turai suna tunanin kakabawa kasar Rasha sabbin takunkuman tattalin arziki masu tsanani saboda murkushe yan hamayya da take yi a kasar.

Aikin shimfada bututun gas na ‘Nord stream 2 Project’ dai zai isar da iskar gas na kasar Rasha ne ga kasashen Turai ta kasar Jamus kuma a cikin farashi mai sauki.

A halin yanzu dai kasashen na turai suna sayan iskar gas ne daga kasar Amurka kan farashi mai tsada sosai.

Amurka bata son aikin ya ci gaba, don zai sanya kasashen turai su dogara ga kasar Rasha don samun makamashi, wanda kuma zai bawa kasar ta Rasha fifiko a kansu ta hanyoyi da dama.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!