​Najeriya:Udofia Ne Zai Horasda D’Tigers Saboda Gasar 2021 Na Kwallon Kwando Ta Nahiyar Afirka

2021-02-01 18:28:10
​Najeriya:Udofia Ne Zai Horasda D’Tigers Saboda Gasar 2021 Na Kwallon Kwando Ta Nahiyar Afirka

Hukumar kwallon Kwando ta Najeriya, wato Nigeriasn Basketball Federation ko (NBBF) ta bada sanarwan cewa mai horaswa ta hukumar Mr Mfon Udofia ne, zai karbi ragamar horaswa da kuma jagorantar kungiyar kwallon kwado ta kasar wato D’Tigers zuwa gasar wasannan kwallon Kwando na shekara ta 2021, ta nahiyar Afirka wadanda za’a gudanar a kasar Tunisia.

Jaridar premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban NBBF Musa Kida yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa a lokacin wasannin na kasar Tunisia dai, masu horasda kungiyar D’ Tigers, Alex Nwora da kuma Mike Brown, ba zasu sami damar zuwa ba, amma tare da Udofia D’ Tigers suna aya samun nasara a wasannin.

Musa Kida ya bayyana cewa Udofia ne zai jagoranci D’Tiger zuwa kasar Tunisia kuma yana da tabbacin cewa zai yi aikin da ya dace na samun nasarar kungiyar kwallon Kwando ta Najierya wato D’ Tigers a wasannin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!