Sojojin Myanmar Zasu Shirya Sabon Zabe

2021-02-01 14:48:25
Sojojin Myanmar Zasu Shirya Sabon Zabe

Sojojin da suka kifar da mulki a Myanmar, sun sanar a wannan Litinin cewa, zasu shirya sabon zabe a kasar bayan kammala cikar wa’adin dokar ta bacin da suka kafa a kasar ta tsawon shekara guda, daga bisani zasu maido da iko ga sabuwar gwamnadin kasar da za a zaba.

Ofishin shugaban kasar ya ayyana kafa dokar ta bacin bayan sojojin kasar sun kifar da gwamnati tare da tsare shugabar gwamnatin kasar, Aung San Suu Kyi, da shugaban kasar U Win Myint, gami da wasu manyan kusoshin gwamnatin kasar.

Sojojin sun bayyana cewa a cikin wa’adin dokar ta bacin da aka kafa, za a kafa hukumar da zata jagoranci shirya zaben kasar kuma za a yi sauye sauye a zaben majalisar dokokin kasar wanda aka gudanar a watan Nuwambar bara.

A sanarwar da aka fitar ta gidan talabijin din kasar na Myawaddy TV wanda sojojin suka karbe ikonsa, ance za a mika ragamar shugabancin kasar ga babban hafsan tsaro na kasar Myanmar, Min Aung Hlaing.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!