Ghana : An Sake Sanya Dokar Kulle Don Dakile Yaduwar COVID-19

2021-02-01 14:46:42
Ghana : An Sake Sanya Dokar Kulle Don Dakile Yaduwar COVID-19

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya sanar da sake kafa dokar kulle domin dakile yaduwar annobar COVID-19 a kasar.

A jawabin da ya gabatarwa ‘yan kasar, da yammcin jiya Lahadi, M. Akufo-Addo ya bayyana cewa, tarukan jama’a da suka hada da na, bukukuwan aure, da shagulgula, da taron gidajen rawa, da tarukan holewa duk an dakatar dasu.

Wuraren shakatawa a bakin teku, da gidajen rawa, da sinima, da sauran wuraren taruwar jama’a duka zasu cigaba da zama a rufe, taron jana’iza ne kadai aka lamince shi ma kada ya zarce mutane 25.

Ya ce, “Asibitocinmu sun cika makil, kuma mun riga mun sake bude cibiyoyin killace marasa lafiya. Yanzu ana samun masu kamuwa da cutar 700 a kowace rana, idan an kwatanta da mutane 200 da ake samu a kullum a makonni biyu da suka gabata," inji shugaban kasar.

Ya kara da cewa, yanayin da ake ciki a yanzu zai iya kara tabarbarewa idan har ba a dauki kwararan matakai daga bangaren gwamnati da kuma su kansu jama’ar kasar ba, domin taimakawa dakile yaduwar cutar.

Kasar Ghana ta ayyana dokar kulle a kasar a karon farko a watan Maris na shekarar 2020, bayan samun rahoton farko na kamuwa da cutar ta COVID-19 a kasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!