CHAN 2020 : Guinea Da Morocco Sun Tsallake Zagayen Daf Da na Karshe

2021-02-01 14:41:47
CHAN 2020 : Guinea Da Morocco Sun Tsallake Zagayen Daf Da na Karshe

A ci gaba da gasar cin kofin nahiyar AFrika, na ‘yan wasan dake murza leda a gida, kasashen Guinea da Morocco sun samu nasarar tsalakewa a zagayen wasan daf da na karshe.

Guinea dai ta lallasa Rwanda da (1-0), a wasan da suka buda yammacin jiya Lahadi.

Ita kuwa Morocco, ta doke takwararta, Zambia da (3-1), a wasan da suka buda a brinin Douala a jiyan.

Sai a ranar 3 ga watan Fabrairun nan ne za’a fafata a wasanin na zagayen daf da na karshe inda Guinea zata kara da Mali, sai kuma Morocco mai rike da kofin na CHAN, da zata fafata da Kamaru mai masaukin baki.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!