​Iran: Ana Ci Gaba Da Bukukuwan Zagayowar Ranakun Nasarar Juyin Musulunci

2021-02-01 10:25:02
​Iran: Ana Ci Gaba Da Bukukuwan Zagayowar Ranakun Nasarar Juyin Musulunci

A kasar Iran ana ci gaba da gudanar da bukukuwan zagayowar ranakun samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar.

A yau ne aka shiga rana ta biyu da fara gudanar da tarukan zagayowar ranakun samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar wanda ya fara daga ranar dawowar marigayi Imam Khomeini a kasar daga gudun hijira.

Bayan dawowar marigayi Imam Khomeini a ranar 1 ga watan Janairun 1979 daga gudun hijirar da ya yi a kasar Faransa, ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Mehrabad da ke birnin Tehran, inda ya gabatar da wani dan gajeren jawabi ga dubban daruruwan mutanen da suka taru a wurin.

Bayan nan marigayi Imam Khomeini ya nufi makabartar Beheshti Zahra da ke kudancin birnin Tehran, inda aka bizne gawawwakin mutanen da suka rasa rayukansu a gwagwarmayar juyin juya halin.

A Beheshti Zahra, marigayi Imam Khomeini ya gabatar da jawabi mai tsawo, inda ya caccaki gwamnatin sarki Shah, tare da bayyana cewa tsarin sarauta a matsayin tsarin da ke gudanar da kasa hakan ya saba wa hankali kuma ba adalci ba ne, domin kuwa al’umma baki daya ba ta da ta cewa a cikin lamarin tafiyar da kasa.

Ya ce al’ummar Iran suna da hakkin su zabi irin tsarin da suke so ya tafiyar da kasar, amma dole ne a kawo karshen tsarin sarauta, wanda zai mayar da sarki shi ne wuka shi ne nama a cikin lamarin kasa da al’umma.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!