Iran Za Ta Zama Ɗaya Daga Cikin Manyan Masu Samar Da Rigakafin Korona A Duniya

2021-01-31 20:14:22
Iran Za Ta Zama Ɗaya Daga Cikin Manyan Masu Samar Da Rigakafin Korona A Duniya

Ministan lafiya na ƙasar Iran, Saeed Namaki, ya bayyana cewar nan da ‘yan watanni masu kamawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta zama ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da suke samar da rigakafin cutar Coronavirus (COVID-19) a duniya.

Saeed Namaki ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a birnin Bam na lardin Kerman da ke kudu maso gabashin ƙasar Iran inda ya bayyana irin raguwar masu kamuwa da kuma mutuwa daga cutar Koronan a Iran a matsayin wata nasara da aka samu sakamakon irin ƙoƙarin da masanar ƙasar suke yi a wannan fagen duk kuwa da yadda cutar take ci gaba da yaɗuwa a wasu manyan ƙasashen duniya.

Ministan lafiyan na Iran ya ci gaba da cewa a halin yanzu dai Iran tana ci gaba da ba da himma ta dukkanin ɓangarori wajen samar da rigakafin cutar ta coronovirus don daƙile yaɗuwarta a ƙasar yana mai cewa a nan gaba kaɗan Iran za ta zamanto daga cikin ƙasashen duniya da suke samar da rigakafin cutar.

Har ila yau kuma ministan ya ce suna ci gaba da sanya ido kan rigakafin da ake yi a wasu ƙasashen don tabbatar da ingancinsu a ƙoƙarin da Iran take yi na sayo wani adadi na rigakafin daga waɗannan ƙasashe, sai dai ya ce Iran ba za ta taɓa bari wata ƙasa ta yi ƙoƙarin gwada rigakafinta a kan al’ummar Iran ɗin ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!