Harin Da Dakarun Iran Suka Kai Kusa Da Jirgin Ruwan Amurka Ya Firgita Jami’an Kasar

2021-01-31 20:11:58
Harin Da Dakarun Iran Suka Kai Kusa Da Jirgin Ruwan Amurka Ya Firgita Jami’an Kasar

Wasu rahotanni da suke fitowa suna nuni da cewa harin da dakarun ƙasar Iran suka kai da wasu makamai masu linzami kan wani waje da ke kusa da inda katafaren jirgin ruwan yaƙin nan na Amurka a yankin Tekun Indiya ya firgita dakarun sojin Amurka.

Wannan lamarin dai ya faru ne a yayin atisayen dakarun na Iran suka gudanar a kwanakin bayan don gwada irin sabbin makamai da kuma dakarun yaƙin da suke da shi inda suka harba wasu makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa ga wani wajen da aka tsara shi da ke kimanin mil 40 daga katafaren jirgin ruwan sannan kuma ya tarwatsa wajen.

Wasu majiyoyin sojin Amurkan sun bayyana cewar wannan nasara da dakarun Iran ɗin suka samu na harba wannan makami mai linzami da kuma yadda ya iya tarwatsa wajen ba tare da Amurkawan sun gano shi ba duk kuwa da kusancin da wajen yake da shi da wannan katafaren jirgin ruwan da Amurkan take taƙama da shi wani lamari ne mai tada hankali ga sojojin Amurkan.

Majiyoyin labaran sun jiyo wasu jami’an sojin Amurkan suna faɗin cewa harba wannan makamin da Iran ta yi bai zo musu da ban mamaki ba, don kuwa suna jiran dakon hakan, to amma abin ɗaga hankalin shi ne irin yadda makamin ya iya tarwatsa wannan wajen da kuma irin yadda na’urorin rada-rada da suke tattare da wannan katafaren jirgin ruwan suka gagara hango wannan makami mai linzamin yayin da aka harbo shi.

Dakarun na Iran da suka gudanar da wannan atisayen dai sun tabbatar da irin ƙarfin da suke da shi na kare ƙasar Iran daga dukkan wata barazana da kuma mayar da martani ga barazanar maƙiya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!