Kamaru Ta Haye Zuwa Matakin Kusa Da Na Ƙarshe A Gasar Kofin CHAN Na Afirka

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Kamaru, mai masaukin baƙi, ta haye zuwa ga mataki na kusa da ƙarshe (semi-finals) a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Afirka ‘yan cikin gida CHAN bayan da ta lallasa abokiyar karawarta ta ƙasar Demokraɗiyyar Kongo (DRC) da ci biyu da ɗaya.
A
wasan da aka buga tsakanin ƙasashen biyu dai a filin wasan na Japoma da ke
birnin Douala, ƙungiyar kwallon ƙafa ta ƙasar Demokraɗiyyar Kongon ne ta
fara zura ƙwallo a ragar Kamarun lokacin da ɗan wasanta mai suna Makabi Lilepo
ya zura ƙwallo a ragar Kamarun a mintuna 22 da fara wasan., to sai dai kuma bayan mintuna 7 dan wasan Kamaru
Yannick Ndjeng ya farke kwallon a mintuna na 29, kafin daga ƙarshe kuma mintuna
uku kafin a tafi hutun rabin lokaci dan wasan kwallon kafa na Kamarun Felix
Oukine Tcheoude ya zura kwallo ta biyu a ragar DRC.
Sakamakon
wasan dai yana nufin kenan ƙasar Kamaru ta haye zuwa ga mataki na kusa da ƙarshe
inda ake sa ran za ta haɗu da ko dai ƙasar Moroko ko Zambiya waɗanda za su kara
a yau ɗin nan.
Wasa
na biyu da za a buga a yau ɗin Guinea Da Rwanda wanda a cikinsu ne ɗaya za ta
wuce zuwa gasar kusa da ƙarshen inda za ta kara da ƙasar Mali wacce tuni take
jira.
A ranar Laraba mai zuwa ne dai za a buga gasar kusa da ƙarshe ɗin filin wasa na Limbe.