​Iran: An Fara Bukukuwan Tunawa Da Kwanaki 10 Na Samun Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci

2021-01-31 14:56:01
​Iran: An Fara Bukukuwan Tunawa Da Kwanaki 10 Na Samun Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci

Jagoran juyin juya halin mulsunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ziyarci hubbaren marigayi Imam Khomeini da ke kudancin birnin Tehran a yau.

Wannan ziyara tana zuwa ne dai a lokacin da ake cikin tunawa da zagayowar ranakun juyn juya halin muslunci a kasar ta Iran da ke cika shekaru 42, inda rana irin ta yau a shekara ta 1979 marigayi Imam Khomeini ya dawo daga gudun hijira da share kusan shekaru 15 yana a waje.

Sannan kuma daidai irin wanann ranar ce ya sanar da cewa za a kafa wata sabuwar gwamnati a kasar Iran bisa ra’ayin al’umma, wadda za ta maye gurbin gwamnatin kama karya ta sarki Shah, inda bayan kwanaki goma da bayar da wanann sanarwa ne aka tabbatar da juyin juya hali na muslunci a kasar.

A yayin wanann ziyara da jagoran ya kai a hubbaren marigayi Imam, ya yi salloli na nafila da kuma karatun kur’ani mai tsarki, sannan kuma ya zagaya sauran kabrukan mutanen da aka bizne a wurin, wadanda suka rasa rayukansu a lokacin gwagwarmayar juyin juya halin musulunci a kasar.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!