Iran: Macron Ba Shi Da Hurumin Shigar Da Saudiyya A Cikin Batun Shirin Nukiliyar Iran

Wasu daga cikin manyan jami’an
gwamnatin kasar Iran sun mayar wa shugaban kasar Faransa Emmnuel macron da
kakkausan martani, kan kiran da ya yin a cewa dole ne a shigar da Saudiyya a cikin duk wata
tattaunawa kan shirin Iran na nukiliya.
Wannan furuci na Macron dai yana
zuwa ne a daidai lokacin da yake kokarin sanya sharuddansa a kan Iran danganec da batun shirinta na
nukiliya, da kuma batun ake yi na yiwuwar komawar Amurka a cikin wanann
yarjejeniya.
Mataimakin shugaban majalisar
dokokin kasar ta Iran Hussain Amir Abdullahian ya bayyana cewa, Macron ko
waninsa, ba su da hurumin saka Saudiyya ko wata kasa ta daban a cikin batun
shirin Iran na nukiliya, bangarorin da suka rattaba hannu kan wannan
yarjejeniya ne kawai suke da hakkin yin duk wata tattaunawa, shi ma a kan abin da
aka rattaba hannu a kansa a baya kawai.
A nasa bangaren ministan harkokin
wajen kasar ta Iran Muhammad Jawd Zarif ya mayar da nasa martanin da cewa,
Macron ya manta yadda aka kulla yarjejeniya kan shirin Iran na nukilya, amma ya
kamata ya kwana da sanin cewa Iran ba za ta karbi wani bangare a cikin duk wata
tattaunawa da ta shafi shirin nata ba.
Haka nan kuma Zarif ya kara da cewa,
dangane da batun tattaunawa a tsakanin
kasashen yankin gabas ta tsakiya kuwa, tun kafin wannan lokacin Iran ta sha
nanata wannan bukata, kuma ta kirayi Saudiyya da sauran kasashen yankin zuwa ga
tattaunawa, amma tasirin Amurka a kansu ne ya hana yin hakan.
015