​An Baiwa Musulmi Mata Jami’an Tsaro Dama Saka Suturar Musulunci A Firka Ta Kudu

2021-01-31 14:46:49
​An Baiwa Musulmi Mata Jami’an Tsaro Dama Saka Suturar Musulunci A Firka Ta Kudu

A kasar Afirka ta kudu kotu ta yanke hukunci da ya bayar da dama ga mata musulmi jami’an tsaro a kasar da su saka lullubi a kansu.

Rahotanni daga kasar Afirka ta kudu na cewa, a halin yanzu kotun kasar ta yanke hukunci da ya bayar da dama ga mata musulmi jami’an tsaro a kasar da su saka lullubi a kansu da ma saka kaya da za su suturce jikinsu a yayin aiki.

Wannan na zuwa ne bayan karar da da wata musulma jami'ar 'yan sanda mai zuna Fatima Issacs ta shigar ne a gaban kotu, bayan da aka hana ta saka lullubi irin na musulunci a yayin aikinta.

An shigar da wannan kara ne tun a cikin shekara ta 2018, inda kotu ta ci gaba da bin kadun lamarin da kuma jin ta bakin lauyoyin wadda ta shigar da kara da kuma alkalai masana tsarin mulkin kasa.

Daga karshe dai a yau kotun ta yanke hukunci, wanda ya baiwa Fatima gaskiya, inda kotun tace ba laifi ba ne domin mata musulmi sun saka lullubi a kansu a lokacin aiki, ko kuma saka sutura da za ta rufe jikinsu daidai koyarwar addininsu.

Musulmi a kasar Afirka ta kudu sun yi farin ciki da wannan hukunci da kotun kasar ta yanke, wanda hakan zai iya ba mata musulmi damar shiga cikin ayyukan jami'an tsaro, wadanda a baya suke gudun shiga aiki saboda hana su saka tufafi daidai da koyarwar addinin musulunci.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!