Najeriya: Mutane 27 Ne Suka Rasa Rayukansu Saboda Cutar Korona A Jiya Jumma’a A Duk Fadin Kasar

2021-01-30 22:05:38
Najeriya: Mutane 27 Ne Suka Rasa Rayukansu Saboda Cutar Korona A Jiya Jumma’a A Duk Fadin Kasar

Yawan mutanen da suke mutuwa sanadiyyar Cutar korona a tarayyar Najeriya ya na karuwa, inda a jiya jumma’a mutane 27 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar wanda kuma wannan shi ne adadin ma fi yawa a yini guda tun bayan bullar cutar a shekarar da ta gabata.

Jaridar Primium times ta Najeriya ta bayyana cewa kafin haka a ranar 15 ga watan Jenerun da muke ciki ma mutane 23 ne suka rasa rayukansu sanadiyar cutar, wanda ya nuna cewa yawan wadanda cutar take kashewa a ko wani yini yana karuwa.

A halin yanzu dai jimillar wadanda cutar ta kashe ya kai 1,577 zuwa sa’o’ii 24 da suka gabata. Cibiyar yaki da cututtuka ta kasa, wato ‘Nigerian Centre for Disease Control’ ko NCDC ta bayyana cewa mutane 1,114 ne suka kamu da cutar ta korona a jiya Jumma’a, a duk fadin kasar. Wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar zuwa 128,674. (19)

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!