Siriya:Fursinonin Kungiyar Daesh A Arewacin Kasar Siriya Sun Fara Bore

2021-01-30 22:01:16
Siriya:Fursinonin Kungiyar Daesh A Arewacin Kasar Siriya Sun Fara Bore

Majiyoyin labarai da dama a kasar Siriya sun bada labarin cewa fursinonin kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh wadanda ake tsare da su a gidan yarin Komat-Al-Bulgar dake gabacin garin Ashadadi a lardin Hasaka suna bore, inda suka kona abubuwa da dama a cikin gidan yarin.

Shafin yada labarai na yanar gizo mai suna “Cibiyar Labaran yaki” na kasar Siriya ya bayyana cewa gidan yarin wanda yake dauke da fursinonin kungiyar Daesh kimani 5000 ya na karkashin kula na wata kungiyar ‘yan ta’addan wacce take samun goyon bayan Amurka, wacce kuma ake kira (Kasad) yake.

Labarin ya kara da cewa mayakan kungiyar kurdawa ta ‘Kasad’ sun yiwa gidan yarin kawayya don hana fursinonin na kungiyar Daesh arcewa daga gidan yarin.

Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta bayyana cewa a cikin watanni uku na karshe na shekarar da ta gabata, an ga sojojin Amurka su na daukar wasu daga cikin mayakan na Daesh don yin amfani da su wajen yakar sojojin kasar Siriya a yankin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!