Kotu FIFA Ta Dagawa Shugaban CAF Kafa Har Zuwa Watan Maris

2021-01-30 21:51:48
Kotu FIFA Ta Dagawa Shugaban CAF Kafa Har Zuwa Watan Maris

Kotun ladabtarwa ta CAS ta dagewa shugaban hukumar wasannin kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF Ahmad Ahmad kafa don bashi damar shiga cikin zaben shugaban hukumar CAF wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Maris na wannan shekarar.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa a jiya Jumma’a ce kotun ladabtarwa ta hukumar wasannan kwallon kafa ta duniya CAS ta bada wannan sanarwan ta kum akara da cewa, saboda barnan da ba za’a iya gyaransa ga Ahmad idan an ci gaba da dakatar da shi ba, ya sa kotun ta dau wannan matsayin, kotun ladabtarwan tana ganin za ta dage masa kama har zuwa bayan zaben ranar 12 ga watan Maris na wannan shekara.

Kafin haka dai hukumar FIFA ta haramtawa Ahmad shiga cikin harkokin wasanni na tsawon shekaru 5 daga watan nuwamban da ya gabata. Saboda wasu laifuffukan wadanda hukumar take zarginsa da su.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!