Najeriya: Kotu Ta Umarci Kamfanin Shell, Ya Biya Manoman Naija Delta Diyya

2021-01-30 14:11:28
Najeriya: Kotu Ta Umarci Kamfanin Shell, Ya Biya Manoman Naija Delta Diyya

Wata kotu a Netherlands, ta bukaci kamfanin hakar man fetur na Shell, ya biya manoman yankin Neja Delta na Najeriya diyya kan gurbata masu gonaki.

Umarnin kotun na zuwa ne bayan shafe sama da shekaru 13 ana shari’a game da batun gurbata muhalli da ake zargin kamfanin na shell.

Kotun ta umarci reshen kamfanin na Shell a Najeriya da ya biyya kan gurbata filayen noma da kuma tabukan ruwa a kauyuka guda biyu wandanda da su ne mutanen kauyukan suka dogara dasu wajen rayuwa.

Haka zalika kotun ta kuma bukaci kamfanin da ya dauki matakai na gaba na kada irin hakan ya sake aukuwa.

Koda yake dai ba’a kai ga yanke nawa kamfanin na Shell zai biya ba a matsayin kudin diyya, amma tuni kungiyoyin fafatukar kare muhalli da al’ummar yankin na Naija Delta suka bayyana shari’ar da gagarimar nasara.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!