​Iraki: An Sake Halaka Wani Adadi Mai Yawa Na ‘Yan Ta’adda

2021-01-30 10:02:02
​Iraki: An Sake Halaka Wani Adadi Mai Yawa Na ‘Yan Ta’adda

Gwamnatin Iraki ta sanar da cewa dakarun kasar sun samu nasarar halaka wasu daga cikin ‘yan ta’addan Daesh a yankin Karku.

Rahotanni daga kasar Iraki na cewa, a jiya Juma’a dakarun hadin gwaiwa na kasar da suka hada da sojoji da kuma dakarun sa kai na Hashd Al-shaabi, sun samu nasarar halaka wasu ‘yan ta’addan ashirin da biyu a farmakin da suke kaddamarwa.

Wannan na zuwa ne a cikin farmakin da sojoji da kuma dakarun sa kai na kasar suka fara kaddamarwa ne a kan ‘yan ta’adda da suke neman sake farfadowa a cikin kasar tare da taimakon wasu kasashen ketare.

Bayan halaka wannan adadi na ‘yan ta’adda, an kuma samu wasu daga cikin kayayyakin da suke amfani da su wajen kai hare-haren ta’addanci, da suka hada da bindigogi da kuma nakiyoyi gami da motoci masu sulke.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!