Italiya Ta Soke Lasisin Sayar Wa Saudiyya Da Makamai Saboda Yakin Da Take Yi A Yemen

Gwamnatin kasar Italiya ta sanar da
soke lasisin sayar wa gwamnatin kasar Saudiyya da makamai, saboda yakin da take
kaddamarwa akan al’ummar kasar Yemen.
Kamfanin dillancin labaran kasar
Italiya AKI ya bayar da rahoton cewa, a yammacin jiya Juma’a, ministan harkokin
wajen kasar Luigi Di Maio
ya fitar da sanarwar cewa, daga yanzu sun dakatar da sayar wa kasar Saudiyya da
makamai har sai abin da hali ya yi.
Ministan
harkokin wajen kasar ta Italiya ya ce, sun dauki wannan matakin ne bisa la’akari
da cewa, ana yin amfani da wadannan makaman ne wajen kisan fararen hula a kasar
Yemen, wanda hakan ya saba wa ‘yan adamtaka, a kan haka sun dakatar da duk wata
mu’mala ta cinikin makamai da gwamnatin Saudiyya.
Ya ci
gaba da cewa, wanann matakin ba zai takaitu da kasar ta Saudiyya ba kawai, zai
shafi har da kasar hadaddiyar larabawa UAE, wadda ita ma tana daga cikin
kasashen da suke kaddamar da wannan yaki a kan al’ummar kasar Yemen, wanda ya
zuwa yanzu ya yi sanadiyyar kashe dubban fararen hula mata da kananan yara,
tare da rusa kasar, da kuma jefa al’ummarta cikin matsanancin hali na rayuwa.
015