​Bangladesh Ta Na Ci Gaba Da Jigilar Yan Gudun Hijiran Rohingya Zuwa Wani Tsibiri Nesa Da Kasar

2021-01-29 20:35:23
​Bangladesh Ta Na Ci Gaba Da Jigilar Yan Gudun Hijiran Rohingya Zuwa Wani Tsibiri Nesa Da Kasar

Gwamnatin kasar Bangladesh ta tura tawaga ta ukku na ‘yan gudun hijira musulman Rohingya, ‘yan asalin kasar Myanmar zuwa wani tsibiri mai suna Bhasan Char cikin tekun Bengal.

Tsibirin ya bayyana a cikin tekun ne shekaru 20 da suka gabata, kuma gwamnatin kasar Bangaladeh ta gina wuraren zama wadanda suka dace ga yan gudun hijira musulman na Rokhingya kimani 100,000.

‘Yan gudun hijirar Rohingya kimani miliyon guda ne suke rayuwa a kusa da kan iyakar kasashen biyu a halin yanzu, bayan bayan da gwamnatin kasar Myanmar ta koresu daga kasarsu.

A yau Jumma’a dai yan gudun hijira 1,778 ne zasu koma Tsibirin na Bhasan Char. Tun watan Decemban da ya gabata ne sojojin kasar na Bangaldesh suka fara jigilar yan gudun hijirar zuwa wannan tsibirin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!