​Gasar Premier League:Liverpool Ta Lallasa Tottenham Spur Da Ci 3-1

2021-01-29 20:28:25
​Gasar Premier League:Liverpool Ta Lallasa Tottenham Spur Da Ci 3-1

A wasannin Premier League wanda da ake gudanarwa a kasar Brutaniya a halin yanzu, kungiyar kwallon kafa ta Livapool wacce ta bakwanci birnin London ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Spurs da ci 3 da 1.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wasan wanda aka gudanar a filin wasani na Tottenham da ke arewacin birnin London, da farko Roberto Firmino dan wasan Liverpool ya saka kwallo a ragar Spurs bayan da Sadio Mane dan kasar Senegal ya tura masa a Karin lokaci, a bangare na farkon wasan.

Sai kuma a minti na 49 dan wasan Spurs, wato Pierre-Emile ya rama kwallo guda, amma daga bayan Sadio Mane ya sake jefa kwallo a ragar Spurs. Da haka kuma aka tashi 3-1 wanda ya bawa kungiyar kwallom kafa ta Livapool matsayin na 4 da maki 37, a yayinda Tottenham ta dawo matsayi na 6 tare da maki 4 kasa da na Liverpool.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!