Rundunar Sojin Afirka Ta Kudu Ta Ɗage Haramcin Sanya Hijab Ga Sojoji Musulmi

Rundunar sojan Afirka ta Kudu ta yi gyara wa tsarin sanya tufafin jami’an sojin don ba da dama ga mata musulmi da suke cikin sojan su sanya ɗan kwali (hijabi) a matsayin wani ɓangare na tufafinsu na soja.
Kakakin
rundunar sojin Afirka ta Kudun, Mafi
Mgobozi, ne ya bayyana hakan a jiya
Alhamis inda ya ce: An yi gyara wa tsarin tufafin sojojin don ba wa mata musulmi damar sanya hijabi a ƙasar hularsu ta
soji.
Batun
ba wa musulmi mata damar sanya hijabin ya taso ne bayan da wata kotun soji ta
janye shari’ar da take yi da wata jami’ar soji musulma Manjo Fatima Isaacs
wacce a baya aka same ta da laifin sanya hijabi a ƙasar hulanta na soji.
A
watan Yunin 2018 ne aka zargi Manjo Isaacs din da laifin bijire wa doka bayan
da jami’in da take ƙarƙashinsa ya buƙace ta da ta cire hijabin nata a lokacin
da take sanye da tufafin sojin.
Manjo Fatima ɗin dai ta shafe shekaru tana shari’a da hukumar sojin don neman an tabbatar mata da ‘yancinta na sanya hijabin, inda daga ƙarshe dai aka amince mata da ta sanya hijabin a ƙasar hularta ta soji.