Shugabannin Larabawa Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Shugaban Tunusiya Kan Shirin Kashe Shi Da Isra’ila Ta Yi

2021-01-29 14:19:46
Shugabannin Larabawa Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Shugaban Tunusiya Kan Shirin Kashe Shi Da Isra’ila Ta Yi

Shugabannin ƙasashen larabawa daban-daban sun nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasar Tunusiya Kais Saeed dangane da ƙoƙarin kashe shi da aka yi ta hanyar amfani da guba da ake zargin Isra’ila ce ta yi hakan.

Fadar shugaban ƙasar Tunusiyan ya sanar da cewa Sarkin Qatar, Tamim Bin Hamad Al Thani, cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da shugaban Tunusiyan, ya sanar da shi goyon bayansa gare shi dangane da wannan ƙoƙari na kashe shi da aka yi.

Har ila yau fadar shugaban ƙasar ta ce shugaban gwamnatin haɗin kan ƙasar ta Libiya Faiz Saraj ya bugo waya wa shugaba Kais Saeed inda ya sanar da goyon bayansa ga al’umma da kuma gwamnatin Tunusiya sakamakon ƙoƙarin kashe Shugaba Saeed ɗin da aka yi.

Fadar shugaban Tunusiyan dai ta sanar da yunkurin kashe shugaban kasar ne mai shekaru 62 a duniya ta hanyar wata wasiƙa da aka aiko masa wacce ta ke ɗauke da guda mai saurin kisa.

Fadar shugaban ƙasar ta ce jami’in da ya buɗe wasiƙar ta shiga wani yanayi na rashin jin daɗi da rashin lafiya sakamakon gubar da aka yi amfani da ita sai dai kuma ta ce babu abin da ya sami shugaban.

Wasu majiyoyi da ‘yan siyasar ƙasar dai sun zargi Isra’ila da hannu cikin wannan ɗanyen aiki.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!