Firayi Ministan Iraƙi Ya Sanar Da Kashe Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ISIS A Iraƙi

Firayi ministan ƙasar Iraƙi, Mustafa al-Kazimi, ya sanar da cewa jami’an tsaron ƙasar sun sami nasarar hallaka Abu Yasir al-Aisawi, mataimakin shugaban ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh (ISIS) a wani harin da aka kai masa.
Firayi
ministan na Iraƙi ya sanar da hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa
na Twitter inda ya ce: Al’ummar Iraƙi dai idan suka yi alƙawari suna cikawa,
don haka kamar yadda suka sha alwashin mayar da martani mai kaushi ga ƙungiyar
ta’addancin Daesh, lalle sun cika wannan alƙawarin.
Daga
nan sai ya sanar da hallaka Abu Yasir al-Aisawi ɗin wanda ya ce yana kiran
kansa a matsayin mataimakin Halifa ko kuma gwamnan Iraƙi na ƙungiyar ta Daesh
yayin wani hari na musamman da jami’an tsaron
suka kai masa.
Firayi minista al-Kazimi dai bai yi ƙarin bayani kan yadda aka gudanar da harin ba, to sai dai a makon da ya wuce ne sojojin Iraƙin suka ƙaddamar da wani hari da suka kira ‘Neman Ɗaukar Fansar Jinin Shahidai’ inda suka sami nasarori da dama kan ‘yan ta’addan.