Iran Za Ta Kafa Na’urorin Tace Uranium 1,000 A Cikin Watanni Masu Zuwa

2021-01-28 21:52:51
Iran Za Ta Kafa Na’urorin Tace Uranium 1,000 A Cikin Watanni Masu Zuwa

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta ce za ta kafa na’urorin tace uranium samfarin IRM2 guda dubu a cikin watanni uku masu zuwa a tashar nukiliyar Natanz.

Da yake sanar da hakan kakakin hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran, Behrouz Kamalvandi, ya ce hukumar ta gama duk wani shirinta kamar yadda jagoran juyin juya halin musulinci na kasar, ya bayar da umarni.

M. Kamalvandi, ya ce duk wadannan ayyukan ana yin su ne da kayayakin da Iran ta kera da kanta, kamar yadda ya fadawa ‘yan jarida yayin ziyarar da shugaban majalisar dokokin kasar, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya kai a tashar Fordow, ranar Alhamis.

A kwanan baya ne Iran, ta sanar da fara tace sinadarin uranium zuwa kashi 20% a tashar ta Fordow, bayan da majalisar dokokin kasar ta bukaci hakan.

Iran, ta kuma yi barazanar rufe tashoshin nukiliyarta ga hukumar hana yaduwar makamman nukiliya ta duniya, IAEA, idan dai Amurka ta yi kunnen uwar shegu game da bukatar dage mata takunkumi.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!