An Zargi Isra’ila Da Yunkurin Hallaka Shugaban Tunisia Da Guba

2021-01-28 21:49:34
An Zargi Isra’ila Da Yunkurin Hallaka Shugaban Tunisia Da Guba

Wasu bangarori a Tunisia, sun fara zargin Isra’ila da hannu a yunkurin kisan shugaban kasar Kais Saied, ta hanyar guba.

Da yammacin ranar Laraba ne kafofin yada labarai Tunusia, suka rawaito lamarin yunkurin kisan shugaban kasar mai shekaru 62, ta hanyar wata wasika da aka sanya wa guda mai saurin kisa, wacce aka aika wa fadar shugaban kasar.

Bayanai daga Tunisiar sun ce babu abunda ya samu shugaban kasar, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.

An bayyana gubar mai hadarin gaske, wacce idan har an shake tana da saurin kisa.

Wata majiya a fadar shugaban kasar ta Tunusia, ta ce wani jami’I ne a fadar shugaban kasar ya bude wasikar mai dauke da gubar, kuma shi ma yana cikin koshin lafiya.

Saidia tuni wasu jiga jigan jam’iyya mai mulki a Tunisia suka fara zargin Isra’ila da hannu a yunkurin kisan shugaba Kais Saied da, saboda yadda ya soki yarjejeniyar da wasu kasashen larabawa suka kulla da Isra’ilar a baya baya nan.

A watan Oktoba na shekarar 2019, yayin muhawarar da aka shirya gabanin zaben shugaban kasar, M. Saied, ya caccaki duk wani yunkuri na kulla alaka da Isra’ila, wanda ya ce kasarsa na cikin yaki ne da yahudawan mamayar, kuma duk wani mahaluki da ya kulla alaka dasu tamakar ya ci amana.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!