Iran Da Georgia Sun Kudiri Anniyar Fadada Alaka A Tsakaninsu

2021-01-28 21:44:37
Iran Da Georgia Sun Kudiri Anniyar Fadada Alaka A Tsakaninsu

Kasashen Iran da kuma Gerogia, sun kudiri anniyar fadada alakar dake tsakaninsu a bangarori da dama.

Wannan bayanin ya fito ne bayan wata ganawa da ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya yi da shugabar kasar ta Georgia, Salomé Zourabichvili, a birnin Tbilissi na kasar ta Georgia a wannan Alhamis.

Shugabar kasar ta Georgia, ta bukaci kara hadin guiwa a tsakanin kasashen biyu musamman ta bangaren jigilar kayayaki a tekun farisa.

Bayan ganawa da shugabar kasar, Zarif, ya kuma gana da manyan jami’an kasar ta Gerogia da dama, inda kasashen biyu suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi alakar kasashen dama batutuwan da suka shafi kasa da kasa dama yankin.

Bayan ganawar kasashen biyu sun jadada anniyarsu ta fadada alaka tsakaninsu musamman ta fuskar tattalin arziki da kuma kasuwanci.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya kuma mika goron gayyata ga shugabar kasar ta Georgia na ta kai ziyara birnin Tehran.

Ziyarar ta Zarif, a Georgia, ita ce ta hudu a ran-gadin da ya kaddamar farkon makon nan a kasashen da suka hada da Azerbaïdjan, Rasha Arménia sai kuma Turkiyya a nan gaba.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!