​Najeriya:Cutar COVID-19 Tana Kara Yaduwa A Cikin ‘Yan Kwanakin Da Suka Gabata A Kasar

2021-01-28 13:17:14
​Najeriya:Cutar COVID-19 Tana Kara Yaduwa A Cikin ‘Yan Kwanakin Da Suka Gabata A Kasar

Mako guda da ya gabata aka samu adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar korona a Najeriya tun bayan bullar a shekarar da ta gabata wato mutum 1,964 a yini guda.

Ton lokacin ne dai, wannan adadin yake sama ya yi kasa, inda a jiya Laraba adadin ya kai mutane 1,861 tare da mutuwar mutane 22.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shafin rahoton cibiyar yaki da cuttuka ta kasa (NCDC) ya na cewa ya zuwa yanzu jimillar mutanen da suka kamu da cutar tun bayan bullarta a shekarar da ta gabata ya kai mutum 126,160. Sannan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar kuma ya kai 1,544.

Daga karshe rahoton ya bayyana cewa cibiyar ta yi wa mutane 1,241,230 gwajin cutar tun farkon bayyar ta a shekarar da ta gabata a duk fadin kasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!