Shamkhani:Iran Ba Zata Amince Da Duk Wani Bangare Da Ya Kwace Iko Da Karfi A Kasar Afganistan ba

2021-01-28 13:15:04
Shamkhani:Iran Ba Zata Amince Da Duk Wani Bangare Da Ya Kwace Iko Da Karfi A Kasar Afganistan ba

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkhani ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba za ta Amince da duk wani bangare da ya kwace iko da karfi a kasar Afganistan ba.

Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta nakalto Shamkahni yana fadar haka a jiya Laraba, bayan ganawarsa ta tawagar kungiyar Taliban ta kasar Afganistan wacce take ziyara a Iran tun ranar Talata.

Tawagar wacce Mullah Abdul Ghani Baradar yake jagoranta, ta zo kasar Iran ne tare da gayyatar gwamnatin kasar, don tattauna batun dawo da zaman lafiya a kasar Afganistan.

Shamkhani ya kammala da cewa gwamnatin kasar Amurka ,wacce take mamaye da kasar Afgansitan tun shekara ta 2001, ba ta son ganin an zauna lafiya a kasar Afaganistan.

Daga karshe Shamkhani ya ce don ne dukkan bangarori, da kabilun kasar Afganistan su hada kansu don kafa gwamnati wacce kowa ya amince da ita.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!