Covid 19:Kasashen New Zealand Da Vietnam Su Ne A Gaba Wajen Nasarar Yaki Da Cutar Korona A Duniya

2021-01-28 13:11:01
Covid 19:Kasashen New Zealand Da Vietnam Su Ne A Gaba Wajen Nasarar Yaki Da Cutar Korona A Duniya

Kasashen New Zealand, Vietnam da kuma Taiwan sune kasashe na farko, na biyu da na uku a jere, wadanda suka fi ko wace kasa a duniya samun nasara wajen yakar cutar korona. Amma kasashen Amurka da kuma Burtaniya suna can kasa a cikin kasashe kimani 100 wadanda aka zaba don sanin nasarorin da aka samu wajien yakar cutar a duniya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto cibiyar ‘The Lowy Institute da ke birnin Sydney na kasar Austriala ta na fadar haka a wani rahoton da ta fitar a yau Alhamis.

Rahoton cibiyar ya kara da cewa an zabi kasashe 98 a duniya don aiwatar da wannan kididdigar, amma ba’a sanya kasar Sin ba, inda cutar ta fara bulla, saboda rashin sahihan bayanai kan yadda cutar take a kasar.

Sauran kasashen duniya da suka yi kokari a wajen yakar cutar ta Korona dai sun hada da Thailand, Cyprus, Rwanda, Iceland, Australia, Latvia da kuma Sri Lanka,

Kasar Amurka dai, itace kasa ta 86 a jerin kasashen, saboda rubu’in wadanda cutar ta kama suna kasar Amurka ne, hakama wadanda suka mutu sanadiyyar cutar.

A halin yanzu dai cutar ta korona ta kama mutane fiye da miliyon 100a duniya, sannan ta kashe kimanin mutane miliyon 2.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!