Manyan Jami’an Iran Sun Yi Watsi Da Barazanar Isra’ila Na Kawo Wa Ƙasar Hari

2021-01-28 09:34:55
Manyan Jami’an Iran Sun Yi Watsi Da Barazanar Isra’ila Na Kawo Wa Ƙasar Hari

Manyan jami’an gwamnatin Iran sun yi watsi da barazanar baya-bayan nan da ‘Isra’ila’ ta yi na kawo hari a kan Iran suna masu cewa hakan wani yaƙi ne kawai na ƙwaƙwalwa da nufin hana Amurka dawowa cikin yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran a 2015.

A ranar Talatar da ta gabata ce dai babban hafsan hafsoshin sojin Isra’ilan Laftanar Janar Aviv Kochavi ya ce sojojin Isra’ilan suna sake dubi kan shirin da suke da shi na kawo wa Iran hari yana mai cewa duk wani ƙoƙarin Amurka na sake dawowa cikin yarjejeniyar nukiliyan babban kuskure ne, yana mai cewa tuni ya ba wa sojojin umurnin su tsara wasu sabbin shirye-shiryen kai hari baya ga waɗanda da man ake da su a ƙas.

Yayin da yake mayar da martani kan hakan, mataimakin shugaban ƙasar ta Iran na farko Eshaƙ Jahangiri ya ce Isra’ila dai ba ta da wani matsayi da zai sanya ta yin magana kan wannan lamarin.

Shi ma a nasa ɓangaren shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasar ta Iran, Mahmoud Vaezi yayi watsi da wannan barazanar da cewa holoƙo da kuma ihu bayan hari ne. Yana mai cewa al’ummomin yankin nan dai sun saba da irin waɗannan kalamai na Isra’ila wanda magana ce kawai ba tare da cikawa ba.

Mr. Vaezi ya ce Isra’ila dai ba ta ƙarfin da za ta aiwatar da wannan barazana don kuwa ta san abin da ke jiranta yana mai cewa dakarun ƙasar ta Iran da suka haɗa da sojoji da dakarun kare juyin juya halin Musulunci suna cikin dukkanin shirin da ya kamata wajen kare ƙasar Iran daga dukkanin wata barazana.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!