Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Nijeriya Zai Iya Tsayawa Takara A Majalisar Ƙoli Ta FIFA
2021-01-28 09:20:05

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Amaju Pinnick ya tsallake matakin farko na fatan da yake da shi na takarar zama memba a majalisar ƙoli ta hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA.
Kwamitin
ɗa’a na hukumar ta FIFA ne dai ya wanke Mr. Pinnick ɗin bayan gagarumin
binciken da ya gudanar a kansa na tsawon lokaci inda daga ƙarshe dai ya sanar
da cewa babu wani abin da zai hana shi tsayawa takarar.
A
baya dai kwamitin ɗa’a ɗin ya fara gudanar da bincike kan shugaban hukumar ƙwallon
ƙafa na Nijeriya ɗin bisa wasu zarge-zarge da ake masa, to sai dai daga ƙarshe
kwamitin bai same shi da wani laifin da
zai hana shi tsayawa takara ɗin ba.
Hakan
dai zai ba wa Mr. Pinnick damar cimma burinsa na zama memba a wannan majalisar
wacce ita ce cibiya ta ƙoli mai ɗaukar matsayi a tsayin hukumar ta FIFA.
A ranar 21 ga watan Maris ɗin nan mai kamawa ne ake sa ran za a gudanar da zaben a birnin Rabat na ƙasar Moroko.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!