Rauhani: Yakin Tattalin Arziki Da Amurka Ta Kaddamar Domin Karya Iran Bai Yi Nasara Ba

Shugaba Rauhani na kasar Iran ya
bayyana cewa, yakin tattalin arziki da gwamnatin Amurka ta kaddamar a kan kasar
Iran bai yi nasara ba.
Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne
yau a lokacin da yake halartar taron majalisar ministocin kasar a birnin
Tehran, inda ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya dangane da dukkanin
matakan da Iran ta dauka na tunkarar takunkuman da Amurka ta kakaba mata.
Ya ce halin yanzu bayan faduwar
Donald Trump, Iran ta kara samun tabbaci kan rashin nasarar takunkuman rashin
kan gado da gwamnatin ta Trump ta kakaba mata, wanda kuma ya gama ya tafi cikin kwandon shara na tarihi.
Dangane da batun matakan da Iran ta
dauka na jingine yin aiki da wasu bangarorin yarjejeniyar nukiliya kuwa,
Rauhani ya bayyana cewa Iran din a shirye take ta koma bisa yin aiki da
yarjejeniyar, matukar sauran bangarorin su ma sun koma yin aiki da ita kamar
yadda aka rattaba hannu.
Haka nan kuma ya kirayi kasashen
kungiyar tarayyar turai da su daina bin salon siyasar harshen damo dangane da
abin da ya shafi wanann yarjejeniya, matukar dai da gaske suke yi kan neman
kubutar da ita daga rushewa.
015