Palestine: Yahudawa Sun Rusa Wani Masallaci A Yammacin Kogin Jordan

Jami’an tsaron yahudawan Isra’ila sun
rusa wani masallacin musulmi Falastinawa da ke cikin yankunan gabar yamma da
kogin Jordan.
Rahotani sun tabbatar da cewa, da
safiyar yau jami’an tsaron gwamnatin yahudawan Isra’ila su kutsa kai a cikin
yankunan Falastinawa da ke yankin Ummu Kissah a gabashin matsugunnin yahudawa ‘yan
share wuri zauna na Yata, inda suka killace yankin baki daya.
Daga bisani yahudawan sun shiga rusa
ginin wani masallaci da ake cikin gina shi, kamar yadda kuma suka rusa wata
makaranta ta firamare mallakin Falastinawa da take kusa da masallacin.
Yahudawan dauke da makamai sun hana
kowa isa wurin, tare da yin barazanar harbin duk wani musulmi da ya nemi isa
wurin domin hana rusa masallacin.
Wurin da aka yahudawan suka tafka
wannan ta’asa yana daga cikin yankuna uku da aka
baiwa Falastinawa a matsayin mallakinsu a
cikin yarjejeniyar Oslo, wanda kuma Isra’ila ta ci gaba da kwace
wadannan yankuna tare da korarar Falastinawa da suke mallakarsu, inda take gina
matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna.
015