Majalisar Dattijan Amurka Na Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Batun Neman Gurfanar Da Trump

‘Yan majalisar dattijan Amurka na ci
gaba da tafka muhawara dangane da bukatar neman gurfanar da Trump da majalisar
wakilai ta mika musu.
Tashar RT ta bayar da rahoton cewa,
a yau Laraba ‘yan majalisar dattijan Amurka na ci gaba da tattauna batun neman
a gurfanar da Trump a gaban kuliya, kan zarginsa da laifin tunzura jama’a da su
yi wa kasa tawaye.
Idan aka tabbatar da hakan a kansa, kotu
za ta tsige shi duk kuwa da cewa ya sauka daga mulki, amma hukuncin zai tsaya a
kan haramta masa rike duk wani mukami na gwamnatin kasar Amurka har karshen
rayuwarsa.
Wasu daga cikin ‘yan majalisar
dattijan daga jam’iyyar Republican sun amince da hakan, amma wasu daga cikinsu ba
su amince ba, inda ake neman amincewar sanatoci 17 kawai daga majalisar
dattijai daga jam’iyyar Republican, domin
samun amincewar kashi 2/3 na ‘yan majalisar dattijai wato mutane 67 daga
cikinsu.
Sai dai wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar
Republican din na da ra’ayin cewa, a sauya salon tuhumar da ake yi wa Trump
zuwa zarginsa aikata ba daidai ba a kan kujerar mulki, wanda hakan ya jawo
tarzoma, maimakon neman tsigewa, wanda kuma hakan yana bukatar amincewar
sanatoci 60 ne kawai a majalisar dattijan Amurka.
Yanzu haka dai Amurkawa sun zura ido da kasa kunnuwansu domin jin irin matakin da majalisar dattijan za ta dauka, bayan da majalisar wakilai ta riga ta dauki nata matsayin, na neman a gurfanar da Trump a gaban kuliya, tare da daukar matakai na hana shi sake rike wani mukami har abada a kasar Amurka.
015