Takht-Ravanchi: Iran Za Ta Mayar Da Martani Mai Kaushi Kan Duk Wata Barazanar Isra’ila

2021-01-27 13:48:02
Takht-Ravanchi: Iran Za Ta Mayar Da Martani Mai Kaushi Kan Duk Wata Barazanar Isra’ila

Jakadan ƙasar Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya, Majid Takht-Ravanchi ya bayyana cewar Iran tana da haƙƙin ta mayar da martani mai kaushin gaske a kan duk wata barazana da Isra’ila za a yi wa ƙasar.

Mr. Takht-Ravanchi, Jakadan Iran ɗin na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniyan, ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a babban zauren MDD inda ya ce: Isra’ila ana ci gaba da amfani da ƙarya, yaudara da murguɗa gaskiya wajen nuna cewa shirin nukiliyan Iran wani shiri ne da ke barazana ga yankin, yana mai cewa Isra’ilan tana yin hakan ne don rufe irin nata shirin da take da shi na ƙera makaman ƙare dangi.

Don haka sai ya ce: Iran tana da haƙƙin mayar da martani mai kaushin gaske ga duk wata barazana ta Isra’ilan ga tsaron ƙasarta.

Jami’in diplomasiyyar na Iran ya ci gaba da cewa: Iran ba za ta taɓa yin wata ƙasa a gwiwa ba wajen kare kanta, sannan kuma za ta mayar da martani ga duk wata barazana ga tsaro da zaman lafiyarta.

Wannan mayar da martani na jakadan Iran a MDD tana zuwa ne a daidai lokacin da babban hafsan sojojin Isra’ilan Laftanar Janar Aviv Kohavi ya sanar da cewa Isra’ilan tana cikin shirin kai wa Iran hari cikin wannan shekarar idan har buƙatar hakan ta taso.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!