Tarayyar Afirka Ta Kirayi Ƙasashen Kenya Da Somaliya Da Su Kai Zuciyarsu Nesa

2021-01-27 13:40:08
Tarayyar Afirka Ta  Kirayi Ƙasashen Kenya Da Somaliya Da Su Kai Zuciyarsu Nesa

Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat, ya kirayi ƙasashen Kenya da Somaliya da su kai zuciyar nesa da kuma nesantar duk wani abin da zai ƙara yanayi zaman ɗarɗar da ake fuskanta akan iyakokinsu.

Moussa Faki Mahamat ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce: Ina ci gaba da bibiyan yanayin kai ruwa rana da ke gudana a kan iyakan Kenya da Somaliya cikin damuwa, don haka ina kiran ƙasashen biyu da su kai zuciya nesa sannan kuma su hau kan teburin tattaunawa a tsakaninsu.

Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirkan ya ce tabbatar da zaman lafiya a kan iyakan Kenya da Somaliya wani lamari ne mai muhimmanci ga zaman lafiyan yankin.

Somaliyan dai tana zargin Kenya da goyon bayan masu ɗauke da makami da suke yaƙar sojojin ƙasar, waɗanda Somaliyan ta ce suna fasa kwabrin makamai ne zuwa ƙasar, duk kuwa da cewa Kenyan ta musanta wannan zargin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!