Araqchi:Iran Zata Tattauna Kan Matsalolin Yankin Tekun Farisa Ne Da Kasashen Yankin Kadai

2021-01-27 09:25:34
Araqchi:Iran Zata Tattauna Kan Matsalolin Yankin Tekun Farisa Ne Da Kasashen Yankin Kadai

Kasar Iran zata tattauna batun yarjejeniyar JCPOA ne kawai da kasashe 5+1, sannan dangane da tsaron yankin tekun Farisa kuma da kasashen yankin kadai.

Kamfanin dillancin rabaran IRNA na kasar Iran ya nakalto mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi yana fadar haka a jiya Talata a kasar Kuwait a lokacinda yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar ta Kuwait Sheikh Ahmad Nasir Almuhammad Assabah.

Labarin ya kara da cewa Araqchi ya yabawa kasar ta Kuwait wacce ta shiga tsakanin don sasanta kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa a tsakaninsu.

Anashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Kuwai ya yabawa Jumhuriyar Musulunci ta Iran kan kokarin da take yi na tattaunawa da kasashen yankin saboda tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!