Siriya: Mamayar Yankunan Laraba Da Isra’ila Take Yi Barazanace Ga Zaman Lafiyan Yankin

2021-01-27 09:08:35
Siriya: Mamayar Yankunan Laraba Da Isra’ila Take Yi Barazanace Ga Zaman Lafiyan Yankin

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Siriya kuma jakadan kasar na din din din a MDD, Bashar Jaafari ya bayyana cewa mamayar da haramtacciyar kasar isra’ila (HKI) takewa wasu yankunan kasashen larabawa barazana ce ga zaman lafiya a yankin Asia ta Kudu.

Kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Siriya ya nakalto Jaafari ya na fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake ganawa da yan jaridu a birnin New York cibiyar MDD.

Mataimakin ministan harkokin wajen na kasar Siriya ya kara da cewa, mamayar har’ila yau ta hana MDD aiwatar da ayyukanta kamar yadda ya dace fiye da shekaru 54 da suka gabata.

Jaafari ya bukaci kwamitin tsaro na MDD ya aiwatar da kuduri mai lamba 560 wanda aka samar a shekara 1974 wanda kuma ya hana HIK kai hare-hare cikin wasu kasashe.

Har’lla yau mataimakin ministan ya bukaci kwamitin tsaron ya aiwatar da kuduri mai lamaba 479 wanda aka samar a shekara 1981 wanda ya luzumtawa HKI dakatar da kame-kamen yan kasar Siriya a yankin duddan Golan da ta mamaye, da kuma dakatar da ginawa yahudawa gidaje a duddan na Golan mallakin gwamnatin kasar Siriya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!