Najeriya : Buhari Ya Yi Wa Manyan Hafsoshin Tsaron Kasar Ritaya

2021-01-26 21:10:26
Najeriya : Buhari Ya Yi Wa Manyan Hafsoshin Tsaron Kasar Ritaya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya yi wa manyan hafsoshin sojin kasar ritaya a wannan Talata.

Matakin a cewar wata sanarwar da mai ba shugaban shawara kan harakokin watsa labarai Femi Adeshina ya fitar ta ce, shugaban ya amince da ritayar manyan hafsoshin sojin.

Buhari ya kuma gode wa hafsoshin sojin masu ritaya tare da yi masu fatan alheri.

Hafsoshin sojin sun hada da babban hafsan sojin kasa Janar Tukur Buratai da babban hafsan sojin sojan ruwa Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da babban hafsan sojin sama Air Marshal Sadik Abubakar, da babban hafsan tsaron kasar Janar Abayomi Olonisakin.

Tuni dai shugaban nada sabbin manyan hafsoshin sojin da za su maye gurbinsu, da suka hada da Janar Leo Irabor, da aka nada babban hafsan tsaro, da Janar I. Attahiru, a matsayin babban hafsan sojan kasa.

Rear Admiral A.Z Gambo, aka nada babban hafsan sojan ruwa sai Air-Vice Marshal I.O Amao, a matsayin babban hafsan sojan sama.

A Najeriya dai an jima da ‘yan kasar ke bukatar shugaba Muhammadu Buhari, da ya sauke manyan hafsohin tsaron kasar bisa zarginsu da gazawa wajen magance matsalar tsaro a kasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!