Kasashen Rasha Da Iran Sun Bukaci A Ceto Yarjejeniyar Nukiliya

2021-01-26 21:08:06
Kasashen Rasha Da Iran Sun Bukaci A Ceto Yarjejeniyar Nukiliya

Kasashen Rasha da Iran, sun mika wani kira a wannan Talata, na ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Wannan bayanin ya fito ne yayin wata ganawa da ministocin harkokin wajen kasashen biyu sukayi a birnin Moscow.

Ganawar jami’an biyu ita ce irinta ta farko tun bayan da shugaba Joe Biden na Amurka ya kama aiki, wanda ake sa ran zai iya dawo da Amurka a cikin yarjejeniyar ta nukiliya.

Tattaunawar ta Moscow, na zuwa ne yan kwanaki kadan bayan da ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bukaci Amurka da ta dagewa kasarsa takunkumi domin juya akalar katobarar da tsohuwar gwamnatin Amurka ta yi musamman na ficewa daga cikin yarjejeniyar ta 2015.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!