​ Najeriya : An Dage Shari’ar Sheikh Zakzaky Har Zuwa 8 Ga Watan Maris

2021-01-26 21:00:39
​  Najeriya : An Dage Shari’ar Sheikh Zakzaky Har Zuwa 8 Ga Watan Maris

Kotun jihar kaduna dake saurare shaidu kan shari’ar da ake wa shugaban kungiyar harkar musulinci a Najeriya, cewa da Sheikh Ibrahim Zakzaky ta dage zaman har zuwa watan maris mai zuwa.

A zaman data yi yau Talata, babbar kotun ta Kaduna ta ce za’a ci gaba da shari’ar a ranakun 8 zuwa 9 ga watan Maris na wannan shekara.

A jiya Litini ne kotun ta fara sauraren shaidu kan shari’ar da ake wa Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenat da ake tsare da yau sama da shekaru biyar.

A wani labari kuma daga Najeriyar, rahotanni sun ce mutum daya ya rasa ransa kana wasu da dama sun jikkata sa’in da jami’an tsaro suka tarwatsa zanga zangar magoya bayan Sheikh Zakzakin a Abuja.

Lamarin ya faru yau Talata a yankin Maitama kusa da ofishin hukumar kula da kare hakkin dan Adam, a inda jami’an tsaron sukayi harbe harbe da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa almajiran Zakzakin a cewar rahotannin.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!