CHAN 2020 : DRC-Kamaru-Mali-Congo.B Sun Wuce A Zagayen Kwata Final

2021-01-26 20:53:22
CHAN 2020 : DRC-Kamaru-Mali-Congo.B Sun Wuce A Zagayen Kwata Final

A ci gaba da gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 'yan wasa masu murza tamaula a gida, wato CHAN, wanda ke gudana a Kamaru a halin yanzu, kasashen Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, da Mali, da Congo Brazzaville da Kamaru mai masaukin baki, sun samu nasarar tsallakewa a zageyn kwata final.

DRC, ta samu nasarar wucewa ne bayan da ta lallasa jamhuriyar Nijar, da ci 2-1 a wasan da suka buga jiya a birnin Yaounde wanda hakan ya sa akayi waje da Nijar a din a gasar.

Ita kuwa Congo-B ta lallasa Libiya ne da 1-0, a gungun B wanda ya bata damar tsallakewa a matakin kwata final.

Sai a ranar 30 ga watan Janairu Kamaru zata karawa da Mali, a wasansu na kwata filal.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!