Ravanchi: Iran Ba Za Ta Yi Komai Ba Har Sai Amurka Ta Dauke Takunkuman Da Ta Dora Mata

2021-01-26 15:05:13
Ravanchi: Iran Ba Za Ta Yi Komai Ba Har Sai Amurka Ta Dauke Takunkuman Da Ta Dora Mata

Jakdan kasar Iran a MDD Majid Takht-Ravanchi ya bayyana cewa Tehran tana jiran sabuwar gwamnatin Amurka ta dage takunkuman zaluncin da gwamnatin da ta shude ta dorawa kasar sannan ta sake dawowa cikin yarjejeniyar JCPOA.

Ravanchi ya bayyana haka ne a jiya litinin a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta NBC, sannan ya kara da cewa gwamnatin kasar Iran ba za ta nuna yi wani abu ba sai in Amurka ta cire mata takunkman tattalin arziki sannan ta koma cikin yarjejeniyar JCPOA, wacce ta fice daga cikinta a shekara ta 2018.

Jakadan ya kara da cewa gwamnatin Amurka tana da zabin yin abinda ta ga dama, amma Iran bata gaggawa kuma ta na da abubuwa da dama da za ta yi idan hakan bai faru ba.

An kulla yarjejeniyar JCPOA ne a shekara ta 2015 tsakanin manya-manyan kasashen duniya 6 da kasar Iran dangane da shirinta na makamashin Nukliya, amma a shekara ta 2018 shugaban Amurka wanda ya shude Donal Trump ya fice daga yarjejeniyar wacce kwamitin tsaro na MDD ta amince da ita, tare da samar da kuduri mai lamba 2231 wanda ya tabbatar da yarjejeniyar.


19

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!