Ramaphosa: Manyan Kasashe Su Kawo Karshen Boye Alluran Riga Kafin Korona

2021-01-26 15:02:18
Ramaphosa: Manyan Kasashe Su Kawo Karshen Boye Alluran Riga Kafin Korona

Shugaban kasar Afirka ta kudu kuma shugaban kungiyar tarayyar Afirka na karba karba yay i kira ga manya manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki su kawo karshen boye alluran riga kafin cutar korona da suke yi.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto shugaba Ramaphosa ya na fadar haka a wani jawabinda ya yi a yau Talata a taron yanar gizo na ‘tattalin arzikin duniya, inda ya kara da cewa duniya tana bukatar hadin kai don yakar cutar korona, don haka bai kamata wasu kasashe su nemi tara alluran riga kafin cutar ta korona fiye da bukatarsu ba.

Daga karshen shugaban ya ce akwai wasu kasashen da suka sayi alluran riga kafin cutar ta korona ninki hudu fiye da abinda mutanen kasashensu ke bukata.

19

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!