Gwamnatin Masar Ta Sanya Sunayen ‘Yan Kungiyar Ikhwan Su 50 Cikin Jerin Sunayen ‘Yan Ta’adda

2021-01-26 14:58:18
Gwamnatin Masar Ta Sanya Sunayen ‘Yan Kungiyar Ikhwan Su 50 Cikin Jerin Sunayen ‘Yan Ta’adda

Ma’aikatar sharia a kasar Masar ta sanya sunayen ‘ya’yan kungiyar Ikhwanul Muslimin 50 cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda a kasar. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin shuwagabannin kungiyar wadanda aka sanya sunayensu cikin ‘yan ta’adda sun hada da Abdul Mun’im Abul-Fath, Mohammad Izzat, Hassan Maliki da kuma Umar Assa’idi.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa ma’aikatar ta shari’a,ta tsawaita sanya kungiyar Ikhwanul Muslimin da wasu masu adawa da gwamnatin kasar su 21 cikin jerin sunayen yan ta’adda a kasar.

Tun bayan juyin mulkin da sujojinkasar suka yi a cikin watan Yulin shekara ta 2013 ne ake kai ruwa rana tsanin sojojin da suka yi juyin mulki da kuma yayan wannan kungiyar wacce take ganin juyin mulki ne sojoji aka yiwa zabebben shugaban kasa Muhammad Mursi a lokacin. Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu tun bayan juyin mulkin.


19

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!